Shugaban gwamnonin jihohin Arewa kuma gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya ce ya kammala tsara sunayen kwamishinonin da zai yi aiki da su a wa’adin mulkin sa na biyu.
Gwamna Lalong ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a bikin rantsar da sakataren gwamnatin jihar Farfesa Danladi Atu da shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Neol Kuryil Dongjur, wanda ya gudanar a gidan gwamnati da ke birnin Jos.
Lalong ya kara da cewa, a farkon mulkin sa ya yi amfanin da sunayen da aka bashi ne wajen nada kwamishinoni, wanda a cewar sa hakan ya haifar masa da matsaloli.
Gwamnan ya kuma bukaci sabon sakataren gwamnatin jihar da shugaban ma’aikatan su yi amfanin da a kwarewar su wajen aiwatar da tsare-tsare da za su kawo sauyi mai ma’ana a fadin jihar.
A
nashi bangaran, sabon sakataren gwamnatin jihar, Farfeso Danladi Atu, ya yaba
wa gwamnan da al’ummar Jihar bisa karamcin da suka yi masu, tare da tabbatar da
cewa, za su gudanar da ayyukan da za su
inganta tattalin arzikin jihar baki daya.
You must log in to post a comment.