Home Labaru Gwamnatin Buhari Ta Bada Izinin Gina Layin Dogo Daga Ibadan Zuwa...

Gwamnatin Buhari Ta Bada Izinin Gina Layin Dogo Daga Ibadan Zuwa Kano

601
0
Layin Dogo Daga Ibadan Zuwa Kano

Gwamnatin tarayya ta bada izinin gina layin dogo na zamani daga Ibadan zuwa jihar Kano a kan kudi dala biliyan 5 da miliyan dari 3.

Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri

Karanta Wannan: Sufuri: Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna Ya Dauki Fasinjoji 1 Da Dubu Dari 5 A Kwana 1000

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya tabbatar da aikin a lokacin  da ya ke bayyana kudirin gwamnatin tarayya na inganta bangaren sufuri a Nijeriya.

Rotimi Amaechi ya ce,  bayan wannan muhimmin aiki, a kwai batun fara aikin gina layin dogon daga garin Fatakwal zuwa Warri, domin inganta harkokin kasuwanci a Nijeriya.