‘Yan Najeriya mazauna Birtaniya sun gudanar da zanga zangar lumana a birnin London domin nuna bacin ran su kan abinda suka kira ci gaba da tabarbarewar tsaro a Yankin arewa sakamakon kashe jama’a babu kaukautawa.
Zanga zangar ta janyo mutane da dama akasarin su ‘yan Najeriyar dauke da allunan dake dauke da rubuce rubuce daban daban da suka hada da ‘Tsaro ne Damuwarmu’, ‘Yin shiru aikata laifi ne’, ‘Mutane nawa za’a sake kashewa’, ‘A ceci arewacin Najeriya’.
Sauran rubuce-rubucen sun hada da ‘Buhari ya gaza cika alkawarin da yayi na tsare Najeriya’, ‘A kawo karshen ayyukan ‘Yan bindiga’ , ‘Ana zubda jini a Najeriya amma Buhari na bacci’ da kuma ‘A ceci arewacin Najeriya’ da dai sauransu.
Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga zangar Fareed Lawal Bello ya shaidawa manema labarai cewa duk da yake ba’a zaune suke a Najeriya ba amma sun damu da halin da take ciki.
Ya kara da cewa shugaba Buhari ko damuwa baya yi wajen zuwa ya jajantawa jama’ar da aka kaiwa hari ko zasu ji sanyin kan lamarin.
Daga cikin wadanda suka yi jawabi harda kuma mawallafin jaridar Daily Nigerian Jaafar Jaafar da Lauya Bulama Bukarti.
You must log in to post a comment.