Home Labaru  Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Ayyuka A Jihar Borno

 Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Ayyuka A Jihar Borno

112
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki Birnin Maiduguri a yau Alhamis inda ya kaddamar da ayyukan ci gaban kasa da gwamnatin jihar ta aiwatar.

A yayin ziyarar shugaba Buhari ya kaddamar da wata babbar cibiya a jami’ar Maiduguri da tagwayen hanyoyi masu tsawon kilomita 10 da gadar sama da kuma wata katafariyar makarantar sakandare.

Har ila yau shugaba Buhari ya ziyarci sansanin sojin sama dake Borno inda ya bukaci Rundunar Operation Hadin Kai ta karasa aikin da take yin a murkushe ‘yan ta’adda da sauran masu tada zaune tsaye a yankin baki daya.

A karshe baiwa jami’an sojin tabbacin cewa ‘yan Najeriya na tareda dasu suna kuma basu goyon baya.

Leave a Reply