Home Labaru Mahara Sun Sace Mutane A Wani Masallaci Dake Jihar Taraba

Mahara Sun Sace Mutane A Wani Masallaci Dake Jihar Taraba

59
0
Yan Bindida

Rahotanni daga garin Tella da ke karamar hukumar Gassol a jihar Taraba sunce wasu ‘yan bindiga sun sace mutane a masallacin garin.

Kafar yada labarai ta Daily Trust ta ruwaito wani ganau na cewa ‘yan bindigar su 12 ne suka yi wa masallacin kofar rago, a lokacin da mutanen suke sallar Isha a ranar Laraba.

‘Yan bindigar sun katse musu sallah tare da tasa keyarsu, amma daga bisani sun sako mutum guda.

Cikin wadanda aka sace harda shugaban masu saida hatsi a yankin Alhaji Hussaini.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Taraba DSP Usman Abdullahi ya tabbatar da kai harin.

Cikin makwanni uku da suka gabata, ‘yan bindiga sun sace sama da mutane 25, yawancinsu ‘yan kasuwa daga sassa daban-daban na jihar ta Taraba.

Tun bayan zafafa hare-hare da sojoji suka yi a jihar Zamfara, ya janyowa mazauna karamar hukumar Gassol rashin zaman lafiya inda ‘yan bindiga ke kai hare-hare da satar mutane domin neman kudin fansa.