Home Labaru ‘Yan Fashi Sun Raunata Joao Cancelo Na Manchester City

‘Yan Fashi Sun Raunata Joao Cancelo Na Manchester City

144
0

Mai tsaron baya na Manchester City Joao Cancelo ya samu rauni a wani farmaki da ‘yan fashi suka kai gidan sa da ke arewacin London a daren alhamis.

Cancelo dan Portugal mai shekaru 27 ya wallafa hoton sa a shafin sa na Instagram wanda ke nuna raunin da ya samu a fuska, inda ya ce ‘yan fashin su hudu sun yi kokarin cutar da iyalin sa dalilin da ya sanya shi rikici da su har ya kai ga sun ji masa ciwo.

Acewar mai tsaron bayan na City ‘yan fashin sun kwace sarkokin sa na zinare dana iyalin sa amma basu cutar da iyalin nasa ba face ciwon da suka ji masa a fuska.

Acewar Cancelo, raunin ko kuma fargabar abin da ya faru a lokacin fashin ba zai karya masa gwiwa wajen bayar da gudunmawar da ta kamata a karawar kungiyar sa ta ranar asabar tsakanin ta da Arsenal karkashin firimiyar Ingila ba.

Daga Juventus ne Manchester City ta sayo Cancelo cikin watan Agustan 2019 yayinda yanzu haka ya ke cikin ‘yan wasan da ke taka rawar gani a cikin tawagar ta Pep Guardiola wadda ke matsayin jagorar teburin firimiya da tazarar maki 8 tsakanin ta da mai biye mata Chelsea.

Tuni dai Manchester City ta fitar da sanarwar da ke tir da farmakin kan mai tsaron bayan nata tare da nuna goyon baya gare shi.

Leave a Reply