Home Labaru Harin Bam: Mutum Hudu Sun Mutu A Pakistan

Harin Bam: Mutum Hudu Sun Mutu A Pakistan

75
0

Wani harin bam ya kashe aƙalla mutum huɗu a birnin Quetta da ke kudu maso yammacin Pakistan.

Rahotanni sun ce an kai harin ne domin tarwatsa wani taron wata jam’iyya ta musulunci wanda aka gudanar a wata makaranta.

An bayyana cewa akasarin shugabannin jam’iyyar sun bar wurin a lokacin da aka tayar da bam ɗin, inda aƙalla mutum 16 suka samu raunuka.

Babu wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin kai wannan harin.

A wani ɓangaren kuma, sojoji sun bayyana cewa an kashe jami’an su huɗu a yayin wata arangama a North Waziristan da ke Pakistan.