Rundunar sojin ruwan Najeriya ta ce a shekara mai zuwa ta 2022, za ta matsa ƙaimi tare da sa ido matuƙa kan manyan jami’anta waɗanda ke haɗa baki da masu satar ɗanyen mai da kuma masu aikata laifuka a cikin teku.
Vice Admiral Gambo, ya bayyana haka ne a lokacin da ake ƙarin girma ga wasu manyan jami’an rundunar.
Babban hafsan sojin ruwa na Najeriya, Vice Admiral A.Z Gambo wanda ya yi gargaɗin, ya ce duk wanda aka kama da laifin haɗa kai da masu aikata laifuka domin yin maƙarƙashiya ga tsarin da rundunar sojin ruwa ta yi, lallai za su gamu da fushin rundunar inda za a hukunta su daidai da yadda doka ta tanada.
Ya bayyana cewa rundunar na iya bakin ƙoƙarin ta wajen kare tattalin arziƙin Najeriya ta hanyar yaƙar masu satar ɗanyen man fetur da masu aika wasu laifuka.
You must log in to post a comment.