Home Labaru ‘Yan Damboa Sun Tabbatar Da Harin Mayakan Boko Haram A Jihar Borno

‘Yan Damboa Sun Tabbatar Da Harin Mayakan Boko Haram A Jihar Borno

11
0

Mazauanan garin Damboa na ci-gaba da tserewa don neman mafaka a garuruwa makwafta sakamakon harin da wasu ‘yan kungiyar Boko Haram su ka kai a ranar Alhamis da ta gabata.

Maharan, wadanda ba a tantance adadin su ba, sun kai harin ba-zata  a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno, inda su ka kone gidaje da dama kamar yadda wata ‘yar asalin garin A’isha Kabu Damboa ta bayyana wa manema labarai.

Jami’an karamar hukumar Damboa da su ka bukaci a sakaya sunan su sun tabbatar da faruwar lamarin, inda su ka ce maharan sun kai harin ne da misalin karfe 5:34 na yammacin ranar alhamis da ta gabata.

Rahotannin farko daga wadanda su ka shaida lamarin sun yi nuni da cewa, maharan sun mamaye helkwatar karamar hukumar, inda galibin mazauna kauyen Damboa ke zaune su ka rika harbin kan mai uwa da wabi.

Lamarin da ya tilasta wa mutane tserewa domin tsira da ran su, tare da kulle kan su cikin gida yayin da maharan su ka cigaba da harbe-harbe.