Home Labaru Mun Fada Cikin Tsananin Talauci Da Mawuyacin Hali Dalilin Zaman Kulle –...

Mun Fada Cikin Tsananin Talauci Da Mawuyacin Hali Dalilin Zaman Kulle – Direbobi

21
0

Direbobin motocin haya da ke birnin Umuahia na jihar Abia, sun yi kira ga kungiyar IPOB ta raba masu kayan tallafi domin rage radadin tsananin talaucin da su ka fada saboda dokar zaman gida dole da ta kakaba a fadin jihar.

Sun ce dokar ta fi shafar bangaren sufuri a jihohi biyar da ke yankin Kudu maso Gabashin Nijeriya, sannan idan mutum ya yi kokarin fitowa ya nemi abinci ko wani abu, ‘yan kungiyar za su tare shi su zazzabga ma shi bulala sannan su kora shi gida.

Mazaunan garin un ce, kungiyar IPOB ta sauya dokar daga zama gida duk ranar Litinin zuwa duk ranar da kotu za ta zauna yin Shari’ar Nnamdi Kanu, amma duk ranar Litini mutane su na tsoron fita saboda gudun kada su sha bulala.

Shugaban kungiyar Direbobin haya na jihar Henry Okezie, ya ce akwai ranar da su ka ce za su fita aiki duk da dokar da aka sanya, amma ba su ji da dadi ba, domin ‘yan kungiyar sun lalata ma su motoci sannan su ka ba wasu direbobin kashi.