Home Labaru Yadda Mayakan IPOB Su Ka Kashe Direbobin Tirelar Dangote 3

Yadda Mayakan IPOB Su Ka Kashe Direbobin Tirelar Dangote 3

79
0

Wasu da ake zargin mayakan kungiyar IPOB, ne sun hallaka direban motar Dangote mai suna Saidu Alhassan, da mataimakan sa biyu da su ka hada da Halliru Mallam da Danjuma Isari a karamar hukumar Orse ta jihar Imo.

Lamarin dai ya faru a ranar Larabar da ta gabata, yayin da direbobin ke hanyar komawa wurin aikin su da ke Obajana a jihar Kogi.

Wata majiya ta ce, maharan sun umarci direbobin su sauka daga motar, bayan sun fahimci ‘yan arewa ne su ka harbe su har lahira sannan su ka babbaka gawarwakin su.

Majiyat ta ce, an tsinci gawarwakin ne kusa da motar, daga bisani aka dauke su aka maida su Obajana.

Jami’an tsaro da ‘yan arewa da masu karya dokar zama a gida dai na ci-gaba da fuskantar hare-haren ‘yan kungiyar IPOB a yankin kudu maso gabas gabashin Nijeriya.