Home Labaru ‘Yan Boko Haram Sun Sace Shugaban CAN A Garin Michika

‘Yan Boko Haram Sun Sace Shugaban CAN A Garin Michika

943
0
Ta’addanci: ‘Yan Boko Haram Sun Sace Shugaban Can A Garin Michika
Ta’addanci: ‘Yan Boko Haram Sun Sace Shugaban Can A Garin Michika

Ana zargin ‘yan ta’addan Boko Haram da kama shugaban kungiyar kiristoci ta Nijeriya CAN, Rabaren Lawal Andimi a garin Michika da ke jihar Adamawa.

‘Yan ta’addan dai, an zarge su da sace Rabaren Lawal ne bayan wani hari da su ka kai Kauyen a ranar Alhamis da ta gabata.

Hakimin Michika Ngida Kwace ya bayyana wa mataimakin gwamnan jihar Adamawa Crowther Seth haka, yayin da ya ziyarce su jim kadan bayan faruwar lamarin, inda ya ce ba a sake jin duriyar faston ba tun da ‘yan ta’addan su ka jefa shi cikin mota.

Ya ce a cikin wata mota kirar Toyota Hilux ce ‘yan ta’addan da ake tunanin ‘yan Boko Haram ne su ka jefa Faston.