Home Labaru Abin Da Igbo Za Su Yi Don Samun Shugabancin Nijeriya – Isa...

Abin Da Igbo Za Su Yi Don Samun Shugabancin Nijeriya – Isa Funtua

484
0
Abin Da Igbo Za Su Yi Don Samun Shugabancin Nijeriya - Isa Funtua
Abin Da Igbo Za Su Yi Don Samun Shugabancin Nijeriya - Isa Funtua

Daya daga cikin makusanta shugaba Buhari, Isma’ila Isa Funtua, ya ce ya zama wajibi mutanen yankin kudu maso gabashin Nijeriya su sauya tsarin siyasar su, matukar su na son shugabancin Nijeriya. 

Sama’ila Isa Funtua ya bayyana haka ne, yayin wata zantawa da gidan talabijin na Arise ya yi da shi a cikin shirin ‘The Morning Show’, inda ya ce ‘yan kabilar Igbo ba su cakuduwa da sauran yankuna ta fuskar siyasa, sun fi so su ware gefe guda su rika harkokin su.

Ya ce Moshood Abiola da ake ganin shi ya lashe zaben shugaban kasa a shekara ta 1993, ya yi nasarar kada Bashir Tofa a jihar Kano ne saboda ya rungumi kowa.

Ya ce dole Inyamurai su shigo a dama da su, ba wai su tsaya a mika masu shugabancin kasa kawai ba, domin mulkin Nijeriya kamfanin karba-karba ne.