Home Labaru Iran Za Ta Gane Kuren Ta Idan Ta Taba Mu – Trump

Iran Za Ta Gane Kuren Ta Idan Ta Taba Mu – Trump

347
0
Iran Za Ta Gane Kuren Ta Idan Ta Taba Mu - Trump
Iran Za Ta Gane Kuren Ta Idan Ta Taba Mu - Trump

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce kasar sa ta shirya kai hare-hare a wasu wurare 52 masu muhimmanci ga Iran idan har ta taba kasar sa.

A cikin wani sakon da ya wallafa a shafin sa na Tuwita, Trump ya ce muddin Iran ta taba Amurkawa ko kadarorin ta, to ba za ta yi wata-wata ba wajen maida martani.

Ya ce a shirye kasar sa take ta sanya kafar wando daya da kasar Iran, wadda ta dade ta na addabar jama’a.

Sakon Trump dai ya na zuwa ne, yayin da kasashen biyu ke ci-gaba ta tada jijiyoyin wuya, bayan Amurka ta kashe babban kwamandan sojin Iran a Iraki Qasem Soleimani a wani harin sama.

A baya dai Trump ya ce, gwamnatin sa ta kashe Soleimani, wanda ya zarga da kitsa hare-haren da Iran ke kai wa kasar sa ne domin guje wa yaki, amma a cikin sakon sa na tuwita, ya ce Soleimani ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane, kuma ya na da hannu a harin da aka kai wa ofishin Amurka a Iraki da ma wasu wurare.