Home Labaru Boko Haram: Sama Da Mutane Miliyan 7 Ke Bukatar Taimako A Arewa...

Boko Haram: Sama Da Mutane Miliyan 7 Ke Bukatar Taimako A Arewa Maso Gabas

402
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bude wani taron kwanaki uku a garin Maiduguri na Jihar Borno, wanda ma’aikatar lura da ayyukan jin-kai da raya al’umma su ka shirya na kyautata dangantaka tsakanin hukumomin tsaro da hukumomin da ke bada agaji a yankin.

Wakilin shugaba Buhari a wajen taron Ministan Tsaro Janar Bashir Magashi mai ritaya, ya ce taron an shirya shi ne domin kara kyautata daganata tsakanin sojoji da jami’an da ke bada agajin gaugawa a arewa maso gabashin Nijeriya.

Ministar ma’aikatar lura da ayyukan jinkai da raya al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta ce dole a kyautata danganta tsakanin al’umma da jami’an tsaro da kuma yin aiki tare don a taimaka wa jama’ar da su ka samu kan su cikin wani yanayi.

Shugaban hukumar Majalisar Dinkin Duniya na Nijeriya Mr. Edward Kallon, ya ce sama da mutum miliyan bakwai ke bukatar agajin gaugawa a arewa maso gabashin Nijeriya, wanda shi ne adadin mafi girma a duniya na mutanen da ke bukatar taimako.