Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane Uku A Jihar Katsina

‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane Uku A Jihar Katsina

867
0
‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane Uku A Jihar Katsina

‘Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da raunata wasu biyu a wani sabon harin da su ka kai kauyen Sabon Layin Galadima da ke karamar hukumar Faskaria jihar Katsina.

Sabon harin dai, na zuwa ne kwana kwan guda bayani ‘yan bindiga sun kashe mutane 47 a kauyukan Danmusa da Safana da Dutsin-Ma a jihar Katsina.

A ranar Litinin din da ta gabata ne mazauna kauyen Sabon Layin galadima su ka tabbatarwa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun dira kauyen da misalin karfe 5 +na yammacin ranar Lahadi.

Mazaunin kauyen sun kara da cewa, ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne a kan babura, sannan sun shafe fiye da sa’a guda su na cin Karen su babu babbaka, kana su ka yi awon gaba da dabbobi masu yawa tare da kone gidajen mutane.

Wani mazaunin kauyen ya ce, daga cikin mutanen da suka kashe akwai wani ma’aikacin lafiya mai suna Sanusi Bello, wanda ya zo garin daga kauyen Unguwar Doka, sauran mutanan biyun sun hada  daSafiyanu Abdullahi da Hassan Sani.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah bai yi karin haske a kan faruwar lamarin ba, sakamakon bai amsa sakon karta kwana da aka aika masa ba.