Home Labaru Kiwon Lafiya NCDC Ta Yi Wa ‘Yan Najeriya 8,000 Gwajin Coronavirus

NCDC Ta Yi Wa ‘Yan Najeriya 8,000 Gwajin Coronavirus

388
0
COVID-19: Karin Mutum 4 Sun Kamu A Najeriya
COVID-19: Karin Mutum 4 Sun Kamu A Najeriya

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC ta yi wa mutum dubu 8 da 3 daga cikin mutane dubu 9 da dari 233 da su ka bukaci a yi masu gwaji cutar coronavirus.

Alkalummar cibiyar NCDC na daran ranar Litinin din da ta gabata sun tabbatar da cewa, kimanin mutane 665 ne su ka kamu da cutar COVID-19 a Nijeriya, matakin da ke nuna cewa cutar ta ratsa jihohi 22 da babban birnin tarayya Abuja.

Haka kuma, NCDC ta ce kasha 3 cikin 100 ne na wadanda su ka kamu da cutar ne suka mutu, yayin da aka sallami mutane 188 daga asibiti.

Jihohin Borno da Sokoto da Abia su na cikin wadanda cutar ta ratsa a daga baya-bayan nan, wanda hakan ke nuna cewa jihohin Nijeriya 14 ne kawai cutar bata leka ba.

A karshe alkalumman cibiyar sun tabbatar da cewa, maza sun fi kamuwa da cutar a Nijeriya, sakamakon yadda kusan kashi 70 na wadanda cutar ta kama maza ne.