Home Labarai ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari Kauyen Jihar Katsina

‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Kazamin Hari Kauyen Jihar Katsina

438
0

Aƙalla manoma 15 su ka rasa rayukan su, yayin wani hari da ‘yan bindiga su ka kai a ƙauyen Gakurɗi da ke ƙaramar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Harin dai ya na zuwa ne, sa’o’i kadan bayan mayaƙan Boko Haram sun yi wa manoma 40 yankan rago a jihar Borno.

Wani mazaunin ƙauyen Gakurɗi ya shaida wa manema labarai cewa, maharan sun halaka manoman ne yayin da su ke gyaran gonakin su don shirya ma zuwan Damina.

Ya ce ‘yan bindigar da su ka je a kan Babura hudu, da farko sun kama hanyar zuwa kauyen Gakurdi, amma da su ka ci karo da manoman sai su ka buɗe masu wuta.

Ya ce lokacin da mutanen ƙauyen su ka an kara da abin da ke faruwa, maharan sun gama ta’addancin sun tsere.

LEAVE A REPLY