Home Labarai Dan Namadi Sambo Ya Nemi Deliget Su Mai Masa Da Kudin Sa

Dan Namadi Sambo Ya Nemi Deliget Su Mai Masa Da Kudin Sa

85
0

Dan tsohon mataimakin shugaban kasa Adam Namadi Sambo, ya bukaci wakilan jam’iyyar PDP da ya ba kowannen su Naira Miliyan biyu su maida ma shi kudaden da ya ba su kafin zaben fidda gwani bayan ya samu kuri’u biyu kacal.

Wata majiya ta ce, Adam Namadi ya yi alkawarin kara ma wakilan Naira Miliyan 1 da rabi bayan an kammala zaben, sai dai shi ne ya kasance dan takarar da ya samu mafi karancin kuri’u.

Wakilan jam’iyyar PDP dai sun samu miliyoyin naira a hannun ‘yan takarar da su ka nuna matukar burin son lashe zaben fiye da abokan takarar su.

A karshe dai Sama’ila ya kada Namadi da Shehu Usman ABG, inda ya samu kuri’u 22, yayin da Shehu Usman ABG ya samu kuri’u 14.

Wakilan sun bayyana yadda Sama’ila Suleiman ya rarraba wa ko wannen su Naira miliyan 3 da rabi zuwa 4, yayin da ABG ya bada Naira miliyan 2 da rabi, sai kuma Adam Namadi da ya ba ma kowane wakili Naira miliyan 2.