Home Labarai Nijeriya Na Bukatar Shugaba Mai Dan Tabin Hankali – Obasanjo

Nijeriya Na Bukatar Shugaba Mai Dan Tabin Hankali – Obasanjo

23
0

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce Nijeriya ta na bukatar shugabanni masu tsananin kishin kasa da kuma daukar matakai masu tsauri, wadanda za su taimaka wajen dawo da kimar ta a idan duniya.


Yayin da ya tarbi Mohammed Hayatudeen da ke neman tsayawa Jam’iyyar PDP takara, Obasanjo ya koka da yadda Nijeriya ta samu kan ta a yau, wajen tabarbarewar tsaro da alaka tsakanin jama’a da kuma rashin jagoranci nagari.


Ya ce abin da Nijeriya ke bukata a yau shi ne shugaba mai tsanani, wanda zai rika daukar matakai masu tsauri kamar mai fama da tabin hankali, yayin da ake bukatar ‘yan Nijeriya su sadaukar da kan su wajen maido ta a kan hanya.

Obasanjo, ya gabatar da matakai hudu da ya ce ya dace wanda zai shugabanci Nijeriya ya samu, wadanda su ka hada da fahimtar yadda kasar ta ke da hangen nesa da kudirin sadaukar da kai wajen rufe ido a yi wa kasa aiki, da kuma daukar matakai masu tsauri ko da jama’ar kasa ba su so.