Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 6 A Jami’ar Abuja

‘Yan Bindiga Sun Sace Mutane 6 A Jami’ar Abuja

96
0

Rahotanni sun bayyana yadda wasu ‘yan bindiga su ka shiga Jam’iar Abuja su ka sace mutane 6, wadanda duk ma’aikatan jami’ar ne da iyalan su.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar ‘yan sanda ta birnin Abuja ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce tuni ta baza jami’an ta domin bin sawun ‘yan bindigar.

Haka kuma, jami’an tsaron sun ce an kara tsaurara matakan tsaro a yankin da jami’ar ta ke.

Daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su akwai Farfesoshi biyu da wasu mutane hudu, yayin da bayanai ke nuni da cewa maharan sun kwashe sama da sa’o’i biyu su na cin Karen su babu babbaka a sashen gidajen manyan malaman jami’ar ba tare da samun dauki daga ko ina ba.

Leave a Reply