Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya roƙi sabbin shugabannin kananan hukumomi da mutane su ka zaɓa su maida hankali wajen yi wa al’ummar su aikin da su ke bukata.
El-Rufa’i, ya kuma taya sabbin shugabannin murna bisa nasarar da su ka samu a zaben kananan hukumomi da ya gudana a jihar Kaduna.
Gwamnan ya bayyana haka ne, a cikin wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafin sa na Facebook, wanda ke kunshe da jawabin sa a wajen rantsar da sabbin shugabannin.
El-Rufa’i, ya kuma gargaɗi sabbin shugabannin kananan hukumomin da cewa, kada su sake su nuna bambanci tsakanin waɗanda su ka zaɓe su da waɗanda ba su zaɓe su ba.
You must log in to post a comment.