Home Labaru Wike Ya Bada Wa’adin Kwana Biyu A Binciki Masu Hannu A Lamarin

Wike Ya Bada Wa’adin Kwana Biyu A Binciki Masu Hannu A Lamarin

12
0

Gwamnan Nyesom Wike na jihar Ribas, ya ba gwamnatin tarayya wa’adin sa’o’i 48 ta yi binicke kan wadanda su ka kai samame gidan mai shari’a Mary Odili.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja, Wike ya ce gwamnati da al’ummar jihar Rivers su na daukar matakai domin tabbatar da cewa an binciko tare da hukunta duk wanda ke da hannu a lamarin.

Gwamna Wike ya kara da cewa, suna zargin akwai wasu da ke yunkurin kashe mai shari’a Mary Odili da mijinta da sauran iyalin su, kuma in da mutanen sun samu nasara babi abin da gwamnati za ta yi illa ta ce za ta binciki lamarin kamar yadda ta saba cewa idan aka hallaka mutane.

Ya ce lamarin ba ya da alaka da ministan shari’a, kuma ya ji dadin yadda Abubakar Malami ya fito ya ce ba ya da masaniya a kan samamen da aka kai.

A karshe ya ce tunda gwamnati ba ta da masaniya a kan lamarin, al’ummar jihar sa sun bada wa’adin sa’o’i 48 a binciko tare da bayyana masu hannu a lamarin.