Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Sace Matar Mataimakin Shugaban Fadar Gwamnati A Jos

‘Yan Bindiga Sun Sace Matar Mataimakin Shugaban Fadar Gwamnati A Jos

76
0

Rahotanni da birnin Jos na cewa, ‘ yan bindiga sun yi garkuwa da matar mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Filato Silas Vem.

A wani harin na daban kuma, ‘yan bindiga sun sace daraktan ma’aikatar lafiya ta jihar Filato Dakta Samuel Audu.

Majiyoyi daga fadar gwamnatin jihar Filato da helkwatar ma’aikatar lafiya sun tabbatar da faruwar lamarin, yayin da wata majiya daga fadar gwamnatin jihar ke cewa tsawon kwanaki uku ke nan ba a san inda matar mataimakin shugaban ma’aikatan ta ke ba.

Majiyar ta cigaba da cewa, matar ta na kan hanyar ta komawa ‘ yan bindiga su ka tare ta, sannan su ka tilasta mata fita daga motar ta a gaban kofar gidan su su ka yi awon gaba da ita, kuma tun daga wancan lokacin babu wanda ya sake ji daga gare ta.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Ubah Ogaba, ya ce hukumar su na da masaniyar sace matar kuma su na kokarin ceto ta, sai dai ya ce hukumar ‘yan sanda ba ta da masaniya a kan sace Darakta a Barkin Ladi.