Home Labaru Bangaren Sanata Aleiro Ya Bude Sabon Ofishin APC A Kebbi

Bangaren Sanata Aleiro Ya Bude Sabon Ofishin APC A Kebbi

89
0

Rikicin shugabancin jam’iyyar APC a jihar Kebbi ya ƙara ƙamari, bayan tsohon gwamnan jihar Sanata Muhammadu Adamu Aleiro ya buɗe wata sabuwar helkwatar jam’iyyar a jihar.

Wannan dai ya na faruwa ne, duk kuwa da ƙoƙarin sasanta rikicin da ke tsakanin ɓangaren sa da na gwamnan jihar Sanata Atiku Bagudu da kwamitin Abdullahi Adamu ya yi.

Bangaren Gwamna Bagudu dai ya bayyana buɗe sabon ofishin a matsayin haramtacce da aka yi ba bisa doka ba, yayin da wasu ke ganin matakin Sanata Aleiro a matsayin wanda zai iya janyo wa jihar Kebbi tashin hankalin siyasa.

Wata majiya ta ce bude ofishin bai gudana kamar yadda aka tsara da farko ba, domin an jibge jami’an tsaro a cikin shirin hana gudanar da shi, lamarin da ya sa tsohon gwamnan tare da magoya bayan sa su ka karkata akala zuwa filin Sukuwa su ka yi taron buɗe ofishin.