Home Labaru Tsohon Shugaban Rikon Kwarya Na Nijeriya Cif Shonekan Ya Rasu

Tsohon Shugaban Rikon Kwarya Na Nijeriya Cif Shonekan Ya Rasu

77
0

Allah Ya yi wa tsohon shugaban kasa na rikon kwarya Cif Ernest Shonekan rasuwa a wani asibiti da ke birnin Legas kamar yadda rahotannin su ka bayyana.

Tsohon shugaban kasar ya rasu ne ya na da shekaru 89 a duniya, kuma shi ne shugaban kasa na rikon kwarya tsakanin 26 ga watan Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamba na shekara ta 1993.

Cif Ernest Shonekan dan asalin jihar Ogun, an kuma haife shi ne a watan Mayu na shekara ta 1936 a Lagos.

Ya yi karatun sa na firamare da sakandare duk a Lagos, daga bisani ya tafi London ya yi karatun digiri a fannin shari’a, sannan ya daɗe ya na aiki da kamfanin United Africa tun daga shekara ta 1964, daga baya ya faɗaɗa harkokin sa a kasuwancin ƙasashen waje da kuma shiga harkokin siyasa.

An dai rantsar da Shonekan a matsayin shugaban ƙasa na gwamnatin riƙon ƙwarya bayan Janar Babangida ya sa hannu a kan dokar da ta bada damar yin hakan.