Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Uku Na Wata Makarantar Kirista A Kaduna

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Uku Na Wata Makarantar Kirista A Kaduna

13
0

‘Yan bindiga sun kai hari wata makarantar Kirista ta ɗariƙar Katolika da ke jihar Kaduna, inda su ka sace ɗalibai uku tare da ji ma wasu da dama rauni.

Wannan dais hi ne hari na baya-bayan nan da ake kai a kan makarantu, inda ake sace ɗalibai domin karɓar kuɗin fansa tare da kashe wasu da kuma ji ma wasu rauni.

Wani mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ya shaida wa BBC cewa, mahara a kan babura ne su ka afka wa makarantar Saint Albert Seminary a garin Kagoma da daddare, inda su ka buɗe wuta tare da sace ɗalibai sannan su ka tsere.

Tuni dai an kai wadanda su ka ji rauni asibiti, yayin da aka fara neman waɗanda aka sace a dajin da ke kusa da yankin.