Home Labaru Majalisa Ta Ba Inec Wuka Da Nama A Kan Batun Tura Sakamakon...

Majalisa Ta Ba Inec Wuka Da Nama A Kan Batun Tura Sakamakon Zabe

14
0
Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu kan dokar yanke hukuncin daurin rai da rai ga masu garkuwa da mutane

Majalisar dattawa ta sake duba kudirin yi wa dokar zabe garambawul, tare da ba hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, damar zaben hanyar da ta fi dacewa domin tura sakamakon zabe.

Wata majiya ta ce, a yanzu hukumar zaben ta na da damar zaben hanyar da za ta yi amfani da ita wajen tura sakamakon zaben.

Majalisar ta kuma amince da cewa, dukkan jam’iyyun siyasa su yi amfani da tsarin kato-bayan-kato wajen zaben ‘yan takarar yayin zaben fidda gwani.

A watan Yulin da ya gabata dai, Majalisa ta ba hukumar sadarwa ta kasa damar tura sakamakon zabe ta yanar gizo, lamarin da ya janyo cece-kuce.