Home Labaru Shugaba Buhari Ya Gargadi Ministocin Sa A Kan Aiki Tukuru

Shugaba Buhari Ya Gargadi Ministocin Sa A Kan Aiki Tukuru

15
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya karanto dokar tarzoma ga ministoci a majalisar ministocin sa da sakatarorin dindindin a dukkan ma’aikatu.

Buhari ya bukaci jami’an su dauki batutuwan aiwatar da ayyukan da aka dora masu da muhimmanci.

Shugaba Buhari, ya ce ya na da mahimmanci jami’an su san cewa, sauke nauyin ayyukan su da muhimmanci zai taimaka wa gwamnati wajen cimma burin ta da alkawurran da ta yi wa ‘yan Nijeriya.

Buhari ya bayyana haka ne, a wajen taron bitar ayyukan ministoci na rabin wa’adin sa da aka shirya domin tantance ci-gaban da gwamnatin shi ke kawowa.

Mai ba shugaban kasa shawara ta fuskar yada labarai Femi Adesina, ya ce Buhari ya bayyana haka ne, yayin da ya ke kaddamar da tsarin gudanar da ayyuka shugaban kasa masu fifiko.

Ya ce tsarin ya fara aiki tun daga watan Janairu na shekara ta 2020, kuma ya ba gwamnati damar bibiyar ayyuka a zahirance, tare da samun bayanan da su ka dace kuma ake bukata.