Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗalibai A Jami’ar Tarayya Da Ke Jihar Nasarawa

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗalibai A Jami’ar Tarayya Da Ke Jihar Nasarawa

206
0

‘Yan bindiga sun sace wasu daga cikin ɗaliban jami’ar tarayya da ke birnin Lafiya na jihar Nasarawa.

Kakakin jami’ar Abubakar Ibrahim ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ɗalibai hudu ne maharan su ka yi awon gaba da su yankin da jami’ar ta ke wato Maraba.

Ya ce ‘ yan bindigar sun farmaki yankin jami’ar ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren ranar Alhamis, inda su ka tasa keyar ɗaliban zuwa wani wuri da har yanzu ba a gano ba.

Abubakar Ibrahim, ya ce Mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Shehu Abdul Rahman ya nuna damuwar sa, tare da yin Allah-Wadai da lamarin, sannan ya bukaci a gaggauta sako ɗaliban da aka sace.

Farfesa Shehu Abdul, ya ce garkuwa da ɗalibai na ɗaya daga cikin abubuwan da ke zama barzana ga ilimi a jihar Nasarawa da ma Nijeriya baki ɗaya.

Leave a Reply