Home Labaru Rayuka Sun Salwanta Sakamakon Hatsarin Mota A Jihar Adamawa

Rayuka Sun Salwanta Sakamakon Hatsarin Mota A Jihar Adamawa

31
0

Akalla Mutane 12 ne su ka rasa rayukan su sakamakon wani mummunan hatsarin da ya auku a babban titin Yola zuwa Mubi a jihar Adamawa.

Wata majiya ta ce, Motoci biyu ne su ka yi taho-mu-gama yayin da su ke dauke da fasinjoji, inda nan take su ka kama da wuta kusa da kauyen Golontabal da ke karamar hukumar Song.

Motocin kuwa sun hada da wata kirar Bas da ke kan hanyar zuwa Yola daga karamar hukumar Uba, da kuma samfurin Toyota da ta nufi Mubi Jabbi Lamba a karamar hukumar Girei.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Adamawa DSP Suleiman Nguroje ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tafi da gawarwakin zuwa asibitin Song, yayin da su ke ci-gaba da binciken asalin musabbabin faruwar hatsarin.