Home Labarai Kara Farashin Mai Zai Jefa Karin ‘Yan Nijeriya Cikin Kunci – Abdulsalami

Kara Farashin Mai Zai Jefa Karin ‘Yan Nijeriya Cikin Kunci – Abdulsalami

60
0

Tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar, ya yi
gargadi a kan kara farashin man fetur da cewa zai kara jefa ‘yan Nijeriya cikin fatara da talauci da mawuyacin hali.

Janar Abdulsalami ya bayyana haka ne, a wajen taron
tattaunawa na shekara-shekara karo na 19 da jaridar DailyTrust
ke shiryawa a Abuja.

Bisa ga dukkan alamu dai nan da dan lokaci gwamnati za ta kara
farashin man fetur daga Naira 162 zuwa naira 302 a kan kowace
lita, sai dai Janar Abdulsalami ya ce rashin aikin yi har yanzu ya
na nan, domin akwai ‘’yan Nijeriya sama da miliyan 18 da ke
cikin fatara da talauci babu gaira babu dalili.

Janar Abdusalami ya kara da cewa, Farashin kayan abinci na ci-
gaba da tashi, ta yadda ‘yan Nijeriya da yawa ba za su iya saye
ba, don haka idan aka kara farashin mai za a jefa miliyoyin ‘yan
Nijeriya cikin fatara da kunci.