Home Home ‘Yan Bindiga Sun Kone Hedikwatar Karamar Hukuma A Ebonyi

‘Yan Bindiga Sun Kone Hedikwatar Karamar Hukuma A Ebonyi

36
0
‘Yan Bindiga Sun Kone Hedikwatar Karamar Hukuma A Ebonyi

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Ebonyi, ta tabbatar da harin da wasu ‘yan bindiga su ka kai wani sashen helkwatar karamar hukumar Ezza ta arewa.

Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun kuma kone kadarori masu tarin yawa yayin harin da suka kai.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Ebonyi Chris Anyanwu ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce an fara gudanar da bincike a kan lamarin.

Ya ce su na sane da harin, amma har yanzu ba su samu cikakken bayani ba, amma ana ci-gaba da bincike domin samun cikakken bayani.

Yayin wani taron manema labarai, shugaban karamar hukumar Ogodo Nomeh, ya ce da yawa daga cikin ‘yan bindigar sun samu raunuka yayin da su ke artabu da jami’an tsaro, sai dai kawo yanzu ba a kama kowa ba, saboda lamarin ya faru ne cikin dare.