Dan Takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya karbi sama da mutane dubu 25 da su ka sauya sheka daga wasu Jam’iyyu zuwa PDP, yayin wani taron ganawa da masu ruwa da tsaki da shugabannin jam’iyyar na yankin arewa maso gabashin Nijeriya.
Gwamnan Bala Muhammad na jihar Bauchi, ya bayyana farin cikin sa a madadin al’ummar jihar, sannan ya ba Atiku tabbacin goyon baya da biyayya daga al’ummar jihar Bauchi.
Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Dr Iyorchia Ayu, ya jinjina wa dandanzon mutanen da su ka tarbi Atiku da tawagar sa a Bauchi, sannan ya yi ta’aziyya ga iyalan gwaman jihar bisa rasuwar dan’uwan sa.
A cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shi ta fuskar yada labarai Aburrasheed Shehu ya raba wa manema labarai, Atiku Abubakar ya gode wa al’ummar yankin arewa maso gabas bisa goyon bayan da su ka nuna ma shi, inda ya bukaci tsofaffi da sabbin ‘yan Jam’iyyar su yi aiki tare domin samun nasarar Jam’iyyar.














































