
Fadar shugaban kasa ta shirya kashe Naira Biliyan 14 da miliyan 800 domin sayen Datar hawa shafukan yanar gizo,da takardu da sauran kudaden da su ka shafi katin waya da na’ura mai kwakwalwa a kasafin shekara ta 2023 da shugaba Buhari ya gabatar.
A cikin kasafin, rahotanni sun ce Data kadai za ta ci Naira Miliyan 67 da dubu 100 a fadar shugaban kasa, yayin da takardu da sauran abubuwa da na’ura mai kwakwalwa za su ci Naira Miliyan 79.
Fashin bakin kasafin, ya kuma nuna cewa za a kashe Naira Miliyan 35 da dubu 900 domin biyan kudin wutar lantarki, yayin da harajin katin tangaraho da ruwan famfo za su ci Naira Miliyan 306 da dubu 200, da Naira Miliyan 6 da kuma Naira Miliyan 40 da dubu 600 bi da bi.
Wata majiya ta ce, daga jimillar kasafin kudin, za a kashe Naira Biliyan 1 da Miliyan 600 a kan ma’aikata, sannan, sannan an ware Naira Miliyan 35 a kan sayen littatafai da jaridu, inda jaridu za su ci Naira Miliyan 26, yayin da littatafai kuma za su lashe Naira Miliyan 8 da dubu 600.













































