Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yar Sanda A Jihar Imo

‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yar Sanda A Jihar Imo

15
0

Wata jami’ar ‘yar sanda ta rasa ran ta, yayin da wasu ‘yan ƙungiyar IPOB su ka kai hari ofishin ‘yan sanda na Umuelemai da ke Jihar Imo.

Kakakin ‘yan rundunar sanda Na jihar Imo Mike Abattam, ya ce Maharan sun afka wa ofishin ‘yan sandan da ke Ƙaramar Hukumar Isiala Mbano ne a ranar Alhamis da ta gabata,

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan bindigar da ake zargin ‘yan ƙungiyar IPOB ne su ka isa ofishin ‘yan sandan, inda su ka jefa Bom a kan rufin ofishin sannan suka fara harbe-harbe.

Ya ce ‘yan sandan da ke ofishin sun maida martani, inda su ka yi nasarar daƙile harin tare da fatattakar maharani, amma an kai jami’in ɗan sanda ɗaya da ya ji rauni asibiti domin ba shi kulawa.