Home Labaru Gwamnatin Tarayya Ta Gano Masu Daukar Nauyin Sunday Igboho

Gwamnatin Tarayya Ta Gano Masu Daukar Nauyin Sunday Igboho

23
0

Ministan shari’a Abubakar Malami, ya ce Gwamnatin tarayya ta gano masu daukar nauyin dan gwagwarmayar kasar yarbawa Sunday Igboho.

Da ya ke jawabi a wajen wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja, Malami ya ce wani kwamiti da gwamnatin tarayya ta kafa ya bankado yadda Sunday Igboho ya samu kudade daga asusun bankuna 43 a wasu bankuna tara.

Ya ce Gwamnatin tarayya ta karbi rahoto a kan masu daukar nauyin Sunday Igboho, inda ta gano shi ne shugaban kamfanin Adesun International Concept Limited.

Ministan ya kara da cewa, an gano Sunday Igboho ya na da nasaba da asusun ajiya 43 a bankuna tara, kuma babban mai daukar nauyin shi wani dan majalisar dokoki ta tarayya ne.

Sunday Igboho, ya karbi jimillar kudi Naira Miliyan 127 da dubu 145 daga hannun masu daukar nauyin sa, a tsakanin ranakun 22 ga watan Oktoba na shekara ta 2013, da 28 ga watan Satumba na shekara ta 2020 ta asusun kamfanin Adesun International Concept Ltd.