Home Labaru Kasuwanci Farashin Man Fetur Zai Tashi Kwanan Nan – IPMAN

Farashin Man Fetur Zai Tashi Kwanan Nan – IPMAN

10
0

Kungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kan su ta Nijeriya IPMAN, ta gargadi gwamnatin tarayya cewa da yiwuwar farashin man fetur ya tashi nan ba da jimawa ba, saboda masu defot sun kara farashi daga wajen su.

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano Bashir Danmalam ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce wasu mamallakan defot-defot masu zaman kan su sun kara farashin man fetur daga Naira 148 zuwa Naira 153 ko 155 a kan lita daya.

Ya ce kungiyar su ta sanar da gwamnati ne don kada a dora wa ‘ya’yan ta laifi idan su ka kara farashin mai saboda ba za su yarda da asara ba.

Bashir Danmallam, ya ce Defot-defot masu zaman kan su, su na kokarin yi wa gwamnatin tarayya zagon-kasa ta hanyar kara farashin mai, duk da cewa gwamnati ba ta kara farashin litar mai ba.

A karshe ya bukaci shugabannin kamfanin NNPC su yi bincike a kan lamarin, domin masu defot sun kara farashi tun daga ranar Juma’ar da ta gabata.