Home Labaru Tilas Nijeriya Ta Cigaba Da Kasancewa Kasa Daya Dunkulalliya – Gbajabiamila

Tilas Nijeriya Ta Cigaba Da Kasancewa Kasa Daya Dunkulalliya – Gbajabiamila

267
0
Tilas Nijeriya Ta Cigaba Da Kasancewa Kasa Daya Dunkulalliya – Gbajabiamila
Tilas Nijeriya Ta Cigaba Da Kasancewa Kasa Daya Dunkulalliya – Gbajabiamila

Kakakin majalisar wakilai  Femi Gbajabiamila ya ce, Nijeriya za ta cigaba da kasancewa a matsayin kasa daya al’umma daya duk runtsi.

Gbajabiamila ya ce ‘yan Nijeriya na da dalilai masu tarin yawa da ya kamata su kasance tare cikin hadin kai da kaunar juna domin cigaban kasar.

Kakakin ya bayyana haka ne a lokacin da wata kungiyar matasan arewa ta kawo masa ziyara a ofishin sa dake Abuja, inda ya ce shugabannin da suka gabata sun yi iya bakin kokarin su game da cikasa Nijeriya,  saboda haka yanzu lokacin matasa ne.

Gbajabiamila ya ce, majalisar dokokin a shirye ta ke domin karbar shawarwari daga kungiyoyin matasa, wadanda hakan zai iya taimakawa wajen samun cigaba a Nijeriya.

Da ya ke magana a kan irin muhimmanci da majalisar sa ke ba matasa, Femi Gbajabiamila ya ce burin majalisar shine samar da hadin kai ga ‘yan Nijeriya.

A nashi bangaran shugaban kungiyar Gambo Ibrahim Gujungu, ya godewa kakakin majalisar bisa kayan tallafin da ya rabawa sansanonin ‘yan gudun hijira da ke jihohin Borno da Katsina da kuma Zamfara.