Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 Tare Da Kona Gidaje A Jihar...

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 10 Tare Da Kona Gidaje A Jihar Filato

82
0

Rahotanni daga jihar Filato na cewa, an kashe aƙalla mutane 10, tare da ƙone gidaje a wani hari da ‘yan bindiga su ka kai a Te’egbea da ke ƙaramar hukumar Bassa.

Kwamishinan yada Labarai na jihar Filato Dan Manjang ya tabbatar wa manema labarai faruwan lamarin, inda ya ce ya zuwa yanzu ba a tantance adadin asarar rayuka da dukiyar da aka yi ba.

Wasu rahotanni sun ce, an kai harin ne a cikin dare zuwa wayewar garin ranar Juma’ar nan, inda ‘yan bindigar su ka buɗe wuta tare da cinna wa gidajen mutane wuta.