Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Kona Gari Tare Da Sace Mutane A Jihar Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kona Gari Tare Da Sace Mutane A Jihar Zamfara

99
0

Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa, Gomman mutane sun tsere daga ƙauyen ‘Yan Ɓuki da ke ƙaramar hukumar Zurmi, bayan wani harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyyar hallaka mutane bakwai.

Wani mazaunin ƙauyen da ya tsere zuwa Gusau, ya ce da misalin karfe 12 na rana ne maharan su ka shiga garin tare da bude wuta, sun kuma shiga gidaje su na fito da mata da kananan yara da maza har da tsofaffi sama da 50, inda su ka yi cikin daji da su bayan sun ƙone masu dukiyar da ba a san adadin ta ba.

Ya ce bayan mutanen da ‘yan bindigar su ka tafi da su, sun kuma kashe mutane bakwai, ciki har da dan’uwan sa uwa daya uba daya mai suna Abdullahi.

Mutumin ya kara da cewa, har cikin daki su ka shiga su ka fito da shi, ya na turjewa amma haka su ka harbe shi a baya da kuma makoshin sa.