Gwamnatin jihar Kaduna, ta ɗage dokar hana amfani da hanyoyin sadarwa na tsawon watanni uku da ta sa a wasu kananan hukumomi tun cikin watan Oktoba.
Rahotanni sun ce, gwamnatin ta ɗauki matakin ne, saboda yawaitar hare-haren ‘yan bindiga a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan ya sanar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce tuni gwamnati ta ba hukumomin da ke da alhaki a kan lamarin umurnin su maida hanyoyin sadarwa a yankunan da abin ya shafa.
Sai dai Gwamnatin jihar Kaduna, ta ce har yanzu dokar hana hawa babuwa da safarar dabbobi da cin kasuwannin mako-mako da haramta saida man fetur a jarkoki ta na nan daram.
You must log in to post a comment.