‘Yan bindiga sun kashe wani dan banga da su ka yi garkuwa da shi mai suna Ohikwo, bayan ‘yan’uwan shi sun biya naira miliyan biyu a matsayin kudin fansa.
An dai yi garkuwa da dan bangar ne a yankin Toto da ke jihar Nasarawa, yayin da ya ke komawa kauyen sa na Atako kimanin makonni uku da su ka gabata.
Wani dan’uwan marigayin da ya tabbatar da lamarin, ya ce iyalai sun yi cuku-cuku sun hada naira miliyan biyu domin biyan fansar sa, amma duk da haka sai da ‘yan bindigar su ka kashe shi.
Ya ce sun kashe marigayin ne bayan sun karbi kudin, saboda sun gano cewa shi dan kungiyar ‘yan banga ne, sai dai Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Nasarawa ASP Ramhan Nansele, ya ce rundunar ta san da zancen sace marigayin ne kawai.
You must log in to post a comment.