Home Labaru An Kwato Boma-Bomai Daga Hannun Mayakan Nnamdi Kanu A Jihar Anambra

An Kwato Boma-Bomai Daga Hannun Mayakan Nnamdi Kanu A Jihar Anambra

140
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra, ta ce an gano wasu Boma-Bomai da aka kera a cikin gida daga hannun ‘yan ta’adda masu goyon bayan Nnamdi Kanu.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka Aderemi Adeoye, ya ce an gano Boma-Boman da su ka hada da Bom na RPG da kuma Gurneti, a wurin da aka kai hari a Afor Nnobi da ke karamar hukumar Idemili ta kudu.

Adeoye, ya ce an yi artabu tsakanin jami’an tsaro da ‘yan bindigar, ya na mai cewa an gano kayayyakin ne a cikin wata jaka da aka bari a wurin da aka kai harin.

Da ya ke bayyana kudirin rundunar na tabbatar da tsaro a jihar, ya ce shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya umarci jami’an sa su tabbatar da kare lafiyar mutane yayin zaben gwamnan da za a yi ranar 6 ga watan Nuwamba.

Ya ce tuni kwamishinan ‘yan sanda na jihar Anambra Echeng Echeng, ya yaba hadin kai tsakanin sojoji da ‘yan sanda da jami’an hukumar DSS da sauran jami’an tsaro domin inganta tsaro a jihar.

Leave a Reply