Home Labaru Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Zabe A Jihar Anambra – Massob

Babu Wanda Ya Isa Ya Hana Zabe A Jihar Anambra – Massob

47
0

Daya daga cikin Kungiyoyi masu fafutukar kafa kasar Biafra MASSOB, ta ce babu wanda ya isa ya hana a gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra ranar 6 ga watan Nuwamba.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, MASSOB ta kuma bukaci hukumar zabe ta kasa ta gudanar da sahihin zaben da babu magudi a cikin sa domin samun zaman lafiya.

Idan dai ba a manta ba, a baya kungiyar IPOB yi barazanar hana gudanar da zaben, inda ‘yan kungiyar su ka rika kai hare-hare a kan jami’ai da gine-ginen gwamnati har ma da sanya wa al’umma dokar hana fita.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan Nijeriyar ta ce ta shirya bada tsaron da ya dace don ganin zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali.