Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda A Jihar Ebonyi

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Yan Sanda A Jihar Ebonyi

12
0

‘Yan bindiga sun kai hari helkwatar ‘yan sanda ta karamar hukumar Ohaukwu a jihar Ebonyi.

Wata majiya ta ce, yayin da maharan su ka kai harin, sun saki duk wadanda ake tsare da su a ofishin ‘yan sandan.

‘Ya bindigar, sun kuma kona wasu motoccin sintirin ‘yan sanda, yayin da wasu jami’an ‘yan sandan su ka tsere da raunin bindiga.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Ebonyi Loveth Odah ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ta na mai cewa kwamishinar ‘yan sanda ta jihar ta isa wurin domin gane wa idon ta.

Lamarin dai shi ne na baya-bayan nan, a cikin jerin hare-haren ‘yan bindiga a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.