Home Labaru Gwamnoni Da Jiga-Jigan ‘Yan Siyasa 7 Da EFCC Ke Bincike A Kan...

Gwamnoni Da Jiga-Jigan ‘Yan Siyasa 7 Da EFCC Ke Bincike A Kan Su

22
0
Hukumar EFCC da ke yakar rashawa ta cafke Hafsat Ganduje uwargidan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje kan zargin rashawa da zambar fili wanda ɗanta ya kai kararta.

Zargin wasu fitattun ‘yan Nijeriya kamar yadda takardun Pandora su ka bayyana, ya sa hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta fara gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.

Takardun dai, wadanda wasu gungun ‘yan jarida na duniya su ka buga, sun zargi wasu fitattun ‘yan siyasar Nijeriya da jami’an gwamnati, kuma tuni an fara binciken su da nufin tabbatar da zargin da ake yi masu.

Takardun Pandora ba su tsaya a kan jami’an gwamnati da ‘yan siyasar Najeriya kawai ba, sun kuma kunshi sunaye da dama na fitattun mutane a kasashe 91.

Daga cikin fitattun ‘yan Nijeriya, galibi ana tuhumar su ne da mallakar kadarorin sirri a kasashen waje, wadanda aka same su ta haramtacciyar ribar harkalla.

Daga cikin wadanda ake zargin dai akwai Peter Obi, Mohammed Bello-Koko da Stella Oduah da Gwamna Abubakar Bagudu da Gwamna Gboyega Oyetola da Bola Tinubu da kuma Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun.