Home Labaru Sabon Rikici Ya Barke Tsakanin Mazauna Jihohin Benue Da Ebonyi

Sabon Rikici Ya Barke Tsakanin Mazauna Jihohin Benue Da Ebonyi

13
0

Rahotanni na cewa, an sanya dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari a karamar hukumar Ado ta jihar Benue, bayan sabon tashin hankalin da ya barke tsakanin wasu mazauna wani kauye da ke yankin.

Wata majiya ta ce, an rasa rayukan mutane tara a garuruwan da ke kusa a yankin da ake rikicin tsakanin kananan hukumomi.

Shugaban Karamar Hukumar Ado James Oche ya sanar da dokar hana fitan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Makurdi, inda ya ce matakin da ya dauka ya dogara ne ga matsalolin tsaro a gundumar Apa da ke karamar hukumar.

Lamarin dai ya biyo bayan sabon tashin hankali a tsakanin yankin al’ummomin karkara da ke kan iyakokin jihohin Benue da Ebonyi.

James Oche, ya shawarci mutane su guji kowane irin yunkurin aikata laifi nan da nan ko kuma su girbi abin da su ka shuka, kamar yadda hukumomin tsaro a shirye su ke domin daukar matakai masu tsauri.