Home Labaru ‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum Ɗaya A Jihar Enugu

‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum Ɗaya A Jihar Enugu

84
0

‘Yan bindiga sun harbe mutum ɗaya, tare da cinna ma wasu gidaje wuta a Jihar Enugu.

Ya zuwa yanzu dai, jam’an tsaro sun isa yankin Greece da wasu yankuna daban-daban na birnin, yayin da wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda mutane ke gudun tsira da rayukan su.

An dai zargi ƙungiyar ‘yan aware ta IPOB da kai harin, yayin da su ke ƙoƙarin tabbatar da dokar hana fita a duk ranar Litinin, sai dai ƙungiyar ta musanta zargin da cewa tuni ta soke dokar da ta kakaba.

Lamarin ya tilasta wa mazauna birnin Enugu rufe shaguna da wuraren harkokin su domin tsira da rayukansu.