Home Labaru Gwamnatin Kano Ta Hana Kananan Yara Zuwa Otal Da Wasu Sabbin Dokoki...

Gwamnatin Kano Ta Hana Kananan Yara Zuwa Otal Da Wasu Sabbin Dokoki A Fadin Jihar

102
0

Jami’an kula da wuraren shakatawa na jihar Kano sun hana ƙananan yara zuwa Otal da shan Shisha da ninkaya a kwatamin ruwa tsakanin maza da mata da kuma auren jinsi a faɗin jihar.

Haka kuma, kwamitin ya sake nazari a kan dokokin da su ka halasta kafa wuraren cin abinci da Otal-Otal da kuma ɗakin taro a jihar Kano.

Shugaban kwamitin Baffa Babba Ɗan-Agundi ya bayyana haka, jim kaɗan bayan fitowa daga taro tare da masu Otal da wuraren cin abinci da ɗakunan taro, inda ya shaida masu ci-gaban da aka samu na dokokin da kuma sabuwar tara da gwamnatin jiha ta tanada, wanda zai taimaka wajen tsaftace wuraren sana’a domin kauce wa aikata ba daidai ba.

Jim kaɗan bayan kammala taron a gidan gwamnati, Gwamna Ganduje ya kaddamar da sabbin motoci sama da 8 domin saukaka aikin kwamitin.

Leave a Reply